An Roƙi Gwamnatin Yobe Ta Sassauta Dokar Hana Walwala A Potiskum

0
8252

Muhammad Sani  Chinade, Daga Damaturu

AN roƙi gwamnatin Jahar Yobe da ta sassauta wa al’ummar garin Potiskum dangane da dokar nan ta hana walwala da ta sa daga ƙarfe 4.00 na yammacin kowace rana zuwa ƙarfe 7.00 na safe saboda halin da aka shiga na taɓarɓarewar harkokin tsaro a ‘yan kwanakin nan  wadda hakan na kawo matuƙar tarnaki dangane da rayuwar al’ummomin da suke rage a garin.

Wannan roƙo dai ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar matasan raya garin Potiskum (PEDA), Alhaji Muktari Adamu Yerima a tattaunawar da suka yi da wakilinmu dangane da wannan hali da aka shiga na matsin rayuwa ga al’ummomin garin na Potiskum.

Shugaban ƙungiyar matasan ya ƙara da cewar, kasancewar wannan doka da aka sa ta yi tsauri ya sa kusan dukkan harkokin kasuwancin da garin na Potiskum ya shahara a kai ya tasamma durƙushewa ganin cewar, jama’a sai barin garin suke yi a kullum ba don komai ba sai don ganin rayuwa ta tsananta a garin don babu isasshen lokacin gudanar da harkokin kasuwanci.

Alhaji Muktari ya ƙara da cewar, baya ga matsalar rayuwa har ila yau kuma mafi yawan al’ummomin da suka bar garin ya zuwa ƙauyukan da ke gefen garin na fama da cutar amai da gudawa tare da kamuwa da zazzabi mai zafi wadda ke shanye jinin duk wadda ya kamu da shi har da kan cewar, kakakin Gwamnan Jahar Yobe ya ƙaryata wannan batu ta kafar yaɗa labaran ƙetare cewar, wai ai ba a bi ta hanyoyin da suka dace ba wajen sanar da ɓarkewar annobar amai da gudawa a sansanonin da ‘yan gudun hijirar da ke ƙauyukan da ke kewaye da garin na Potiskum suke, alhali ƙungiyar su ma ta shiga sahun masu taimaka wa waɗanda ke fama da waɗannan cututtuka.

Don haka ne shugaban ƙungiyar matasan raya garin na Potiskum (PEDA) ya roƙi mai girma Gwamna Ibrahim Geidam na Jahar ta Yobe da ya kawo ɗauki ga al’ummomin da ke fama da cututtukan da ya lissafta, kan kuma ya taimaka ya sa a rage masu tsawon lokacin da aka sa masu kasancewar a halin da ake ciki harkokin na tsaro sun fara inganta a garin na sun a Potiskum.

Ya kuma roƙi al’ummomin da suka kaurace wa garin da su dawo don lamura sun fara inganta a garin kana su ci gaba da addu’ar Allah (SWT) ya samar masu da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta yadda harkokin rayuwar yau da kullum za su dawo kamar yadda suke a da.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here