An Yi Kira Ga Gwamnatin Adamawa Ta Gyara Hanyar Mayoime Wafango

0
1337
  1. A masagala, Daga Benin

AN yi kira ga Gwamnatin Jahar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Admiral Murtala Nyako da ta gyara hanyoyi daga garin Mayel Kohi zuwa Mayoine Wafango da kuma hanyar Boggare zuwa garin Modibbo Buba zuwa ta Dangana da babbar hanyar Ngurore sai kuma hanyar wadda ta taso daga garin Kiri Wendu zuwa Mayel Saganare yankunan garuruwan da suke a cikin ƙaramar hukumar Fufore ta jahar.

Ɗan kasuwa a kasuwar garin Yola, Alhaji Usmanu Ciroma Wuro Laide ne, ya yi wannan kiran a kwanakin baya a cikin wata zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin Jahar Adamawa.

Ɗan kasuwan ya ce ya tabbatar idan har gwamnati ta gyara waɗannan hanyoyi zai taimaka wajen inganta tattalin arziƙi na yankunan da kyautata jin daɗin rayuwar al’umma na garuruwan yankunan ta yadda za su iya samun damar gudanar da harkokinsu na kasuwanci da sauransu domin ana samar da ɗimbin amfanin gona da dabbobi a waɗannan yankunan.

Daga nan kuma sai ɗan kasuwan ya yi kira ga shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Fufore, Mista Yohanna A. da ya taimaka wajen gina kasuwa tare da tashar mota a garin Mayoine Wafango da ci gaba da inganta makarantar sakandare da ke garin da sauran makarantu a yankin.

Kuma ɗan kasuwan, Alhaji Usmanu Ciroma ya buƙaci al’ummar yankin da su duƙufa wajen ciyar da ilimin zamani da na addini gaba a yankin, ya ce yin haka shi ne babban jari kuma madogara na sanya yankin ya samu ci gaba mai ma’ana.

Da ya juya a kan batun kyautata ɗabi’u da bunƙasa zaman lafiya a jahar kuwa ya buƙaci al’umma Jahar Adamawa da su bai wa gwamnati haɗin kai da goyon baya a game da shirinta na tabbatar da zaman lafiya ta ɗore a jahar. Ya ce a ƙoƙarta wajen gaggauta samar da hukuma game da duk wani da aka gani yake neman kawo fitina ko yana daure wa masu tada kwance tsaye a jihar,” inji shi’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here