Majalisar Tarayya Ta Ƙalubalanci NAHCO

0
8089

KWAMITIN majalisar wakilai kan harkokin Ƙasashen waje ya nuna ɓacin ransa da damuwarsa kan mutuwar ‘yan Najeriya 44 a Ƙasa mai tsarki a lokacin gudanar da aikin hajjin 2012, wanda ta bayyana shi a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

Shugabar kwamitin, Nnenna ELendu-Ukeje da sauran mambobin kwamitin, sun nuna matuƘar damuwarsu a lokacin da hukumar aikin hajji ta Ƙasa ta kare kasafin kuɗinta na shekarar 2013.

Ukeje wacce ta fito daga Jahar Abiya, kuma ‘yar jam’iyyar PDP, ta ce alƘaluman sun yi yawa, kuma abin dubawa ne.

Ta alaƘanta abin da cewa, akwai zargin rashin tsaftataccen muhalli waɗanda mata ‘yan Najeriya musamman suka tsinci kansu a ciki, a lokacin aikin hajjin da ya gabata.

A don haka ta umarci hukumar ta yi gaggawar miƘa cikakken rahoto kan yadda aka gudanar da ɗaukacin aikin hajjin.

Ta ce rahoton dole ne ya Ƙunshi cikakken rahoto da gamsasshen bayani a kan maganar mutuwar ‘yan Najeriya 44 da wahalhalun da suka fuskanta a aikin hajjin.

Ta kuma taya hukumar murna bisa ga nasarar da ta samu a aikin hajjin, musamman kan maganar magance matsalar muharami da wasu mata suka fuskanta, inda da yawansu aka dawo da su gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here