Jam’iyyar ACN Ta Kuros Riba Ta Zargi Uwar Jam’iyyar

0
1268

AHMAD ABDUL, Daga Kalaba

JAM’IYYAR ACN a Jahar Kuros Riba ta zargi uwar jam’iyyar ta ƙasa da nuna wa wannan reshe saniyar ware da kuma mayar da su baya ga danginsu.

Shugaban jam’iyyar ACN na Kuros Riba, Hillard Eta ne ya bayyana cewa, manema labarai halin da suka tsinci kansu a Kalaba.

Duk da kasancewa jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Lai Mohammed ya rabe masu tsakanin aya da tsakuwa game da matsalolin da suke fuskanta, ya ce “idan  kun fahimce mu, matsalar kuɗi ce ta addabi jam’iyyarmu har ta kai gargara da ba za mu iya biyan buƙatun ofisoshinmu na faɗin ƙasar nan  ba wai an mayar da ku saniyar ware ba ce”.

A bayanin cewa, sauran jam’iyyar adawa in ban da ACN babu wani mai ofisoshi a ƙasar nan da suke motsawa.

Ƙarshe ya nemi ilahirin ‘ya’yan jam’iyyar a Kuros Riba su daɗa haƙuri a kan naɗa komai mai wucewa ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here