Malamai Da Fastoci Su Yi Koyi Da Fasto Yohanna Buru — Yusuf Idris

0
1417

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI, Daga Kaduna

AN yi kira ga ɗaukacin malaman addinin Musulunci da na Kirista da su yi koyi da irin ayyukan farfaɗo da lamarin zaman lafiya da ƙaunar juna kamar yadda lamarin yake a da can tun asali.

Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida reshen Jahar Kaduna, Kwamared Yusuf Idris ya bayyana hakan a Kaduna jim kaɗan bayan kammala taron cin abinci jim kaɗan bayan kammala taron cin abincin rana da Fasto Yohanna D. Y. Buru, ya shirya wa manema labarai a gidansa da ke unguwar rukunin gidajen ma’aikatan kamfanin wayar sadarwa da ke Sabon Tasha a cikin garin Kaduna.

Kwamared Yusuf Idris ya ce, haƙiƙa ayyukan da Fasto Yohanna D. Y. Buru yake aiwatarwa domin ganin an soma fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista lallai abin a yaba ne da ya zama dole a yi kira tare da faɗakarwa ga ɗaukacin malaman addinin Islama da kuma na Kirista kan su tabbatar sun yi koyi da wannan jangwarzo da ke ƙoƙarin tallafa wa ɗaukacin al’umma baki ɗaya.

“Saboda ga duk wanda ya san yadda lamarin zaman lafiya yake a da can tsakanin Musulmi da Kirista lallai idan mutum ya zauna ya dubi yadda lamarin yake a halin yanzu, ya san akwai abin baƙin ciki ƙwarai. Don haka idan an sami wanda ya tashi yana ƙoƙarin sai bara ta dawo bana game da zaman lafiya a cikin garin Kaduna ya zama wajibi a yi masa jinjinar ban girma a kuma taya shi wannan aiki na ciyar da ƙasa tare da al’ummarta ga baki ɗaya”.

Ya ƙara da cewa, yadda Fasto Yohanna yake yi zai faɗakar da jama’a tare da hana duk wani mai yin aikin jagorantar jama’a da sunan addini su kasa karkatar da jama’a.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Fasto Yohanna D. Y. Buru, bayyana matuƙar farin cikinsa ya yi bisa yadda manema labarai suka amsa goron gayyatar da ya aika masu, abin da ya bayyana da cewa, babu wani da zai sami cimma wata nasara ba tare da samun haɗin kai daga gare su ba. “Wannan aikin farfaɗo da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista na fara shi ne a watanni 6 da suka gabata amma tare da ƙoƙarin ‘yan jaridu lamarin ya kai duk inda ba a yi tsammani ba kamar an yi shekaru ana yi, don haka kowa ya bayar da gudunmawarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here