Ƙungiyar NASSI Ta Samar Wa Matasa Miliyoyi Aikin Yi A Najeriya

0
9472

JABIRU A. HASSAN, Daga Kano

SHUGABAN Ƙungiyar  masu Ƙananan masana’antu (NASSI) reshen Ƙaramar hukumar Gwale da ke Jahar Kano, Malam Kamaludeen Adamu Ɗiso ya bayyana cewa, a yanzu haka sama da miliyoyin ‘yan Najeriya ne suka amfana daga wannan Ƙungiya cikin shekara talatin da biyar da kafata.

Ya ce babban maƘasudin kafa wannan Ƙungiya shi ne samar wa matasa maza da mata aikin yi da kuma dogaro da kai da kawar da zaman kashe wando ga matasa.

Da yake zantawa da manema labarai a Kano, ya ce sanin kowa ne cewa,  matasa su ne Ƙashin baya, kowace gwamnati domin irin gudunmawar da suke bayarwa wajen kawo ci gaba da kuma bunƘasa tattalin arziƘin Ƙasa domin duk gwamnatin da ba ta da goyon bayan matasa wannan gwamnati tana cikin tsaka mai wuya.

Kamaludeen Ɗiso ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ci gaba da bai wa wannan Ƙungiya tallafi domin ci gaba da ayyukan alheri ga matasa maza da mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here