Gwamnatin Sakkwato Ta Bayar Da Zakka Da WaƘafi Ga Mutane 6,443

0
8950

Musa lemu, Daga Sakkwato

Gwamnatin Jahar Sakkwato ta bayar da zakka da waƘafi ga al’ummar da abin ya shafa da yawansu ya kai 6,443 na watannin Oktoba da kuma Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Shugaban kwamitin zakka da waƘafi na jahar, Alhaji Lawal Mai doki ya bayyana haka ga wakilinmu da ke Sakkwato a jiya, Laraba.

Alahji Lawal Maidoki ya ce gwamnatin jahar, ta bayar da zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 83 da Naira dubu 76 domin rabawa ga waɗanda abin ya shafa.

Ya ce har yanzu gwamnatin jahar ba ta yi Ƙasa a gwiwa ba wajen raba Naira dubu shida da ɗari biyar a dukkan Ƙarshen wata domin rabawa ga musakai da sauran waɗanda abin ya shafa.

Alhaji Lawal Maidoki ya ce ana raba waɗannan kuɗaɗen ne kamar yadda doka ta tsara bayan an tantance kowa kafin wani ya amfana da wannan zakka. A inda kowane mutum zai amfana da kuɗi Naira 13,000 na waɗannan watanni biyu.

Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewa, dukkan wanda aka yi yunƘurin ba shi zakkar kuɗi Ƙasa da Naira 13,000 ya kai rahoto ga kwamiti ba tare da karɓar ko kwabo ba.

Alhaji Maidoki ya ce bayar da zakkar yana nuna irin tausayawar gwamnatin jahar ne dangane da rage wasu wahalu da wasu marasa Ƙarfi ke fuskanta, tare da rage yawan barace-barace a bisa kan titi.

Daga Ƙarshe, Maidoki ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da masu bayar da zakka da kuma taimaka wa al’ummar da suka kamata a taimaka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here