Sarakuna Sun Nemi A Janye Shingayen Jami’an Tsaro A Kaduna

0
2448

BALARABE JUNAIDU NUHU, Daga Kaduna

MAJALISAR sarakuna ta Jahar Kaduna ta buƘaci gwamnatin jahar da ta duba tsarin shingayen jami’an tsaron da aka kakkafa a wurare daban-daban a jahar don yin gyara ta yadda al’amura za su inganta domin kauce wa muzguna wa waɗanda ba su ji, ba su gani ba.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dokta) Shehu Idris, kuma shugaban majalisar sarakuna na Jahar Kaduna, ne ya bayyana haka ga menama labarai jim kaɗan bayan da suka kammala taronsu na sarakunan jahar, a ɗakin taro da ke harabar majalisar dokokin Jahar Kaduna a shekaranjiya, Talata.

Shugaban majalisar sarakunan ya Ƙara da cewa, “mun ɗan nuna damuwa ga hukumar ‘yan sanda ta yadda ake samun rahotannin muzguna wa wasu waɗanda ba su da wani laifi a wajen binciken, inda muke so su yi bincike da kyau kuma su yi gyara, sannan ya ce ire-iren wannan ɗabi’ar baya nuna ci gaba a sha’anin tsaron”.

Dokta Shehu Idris ya kuma buƘaci gwamnati da ta sa ido sosai don tabbatar da dukkan masu laifi an gurfanar da su a gaban Ƙuliya kuma an zartar masu da hukunci inda ya ce “za a kama mai laifi sai an kai shi gaban Ƙuliya an yi mashi tarar Naira dubu 100, sai ya biya a sake shi, miliyoyin da ya sace kuma ya ci gaba da sharholiyarsa bayan an sake shi, har ma ya riƘa yin dariya ga waɗanda suka kama shi, kuma ya koma ya ci gaba da aikata wannan laifin.

Mai Martaba Sarkin Zazzau ya kuma buƘaci gwamnan Jahar Kaduna da ya kai kuka ga gwamnatin tarayya domin Ƙara yawan jami’an ‘yan sanda inda ya ce ‘yan sandan da ake da su sun yi Ƙaranci matuƘa, sannan ya buƘaci da a ba su lambobin wayar tarho na jami’an tsaro ta yadda za su sanar da su da wuri da zarar an sami wani matsala a masarautunsu.

Sun taya Gwamna Mukhtar Ramalan Yero da mataimakinsa, Ambasada Nuhu Nyam Audu Bajoga murna tare da yin addu’a Allah Ya yi masu jagora.

A nasa jawabin jim kaɗan bayan da sarakunan suka ziyarce shi a fadar gwamnatin jahar, Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ya sha alwashin zai duba wannan matsalar na shingayen jami’an tsaron, inda ya ce “insha Allahu batun shingayen jami’an tsaro za mu duba tare da jami’an tsaro mu ga abin da ya kamata a yi don kawo gyara”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here