WaƘar Tsumagiyar Kan Hanya (I)

0
8719

1. Yunwa halitta ce ita ma Allah ne ya yi ta,

A duk inda ya so a nan ne za a riƘa ganinta.

 

 1. Isarta Ƙasar Nijar nufi ne na sarkin da ya yi ta,

Nijar ba a kasuwa ba ta je ta sayota.

 

 1. Kamata a tausaya wa duk wanda yake da buƘata,

Mu zam muna tunawa da zancen jalla mai wadata.

 

 1. Yunwa a can cikin ciki ne take takawa kowa rawarta,

Akwai wasu ‘yan dalilai da ke yawan haddasa ta.

 

 1. Na farkonsu idan ruwan sama ya kasa yin yawaita,

Ma bi masa tsuntsaye da farin dango suna haddasa.

 

 1. Na ukunsu karancinsu na duke yana sawa a ganta,

A nan ma takan zo ta taka mana ‘yar rawarta.

 

 1. Na huɗunsu talauci yana taimaka wa aukuwarta,

HaƘiƘa rashin kuɗi ma yana sa wa mu fakirai mu sami jinta.

 

 1. Na biyar zaizayar Ƙasa tana haddasa aukuwarta,

Da zarar Ƙasa ta bata shuka takan sami damuwarta.

 

 1. Duk mu ne muka ja wa kanmu dalilin samuwarta,

A inda muka ki ji muka ci ‘ya’yan iccen da aka haramta.

 

 1. Wannan rashin ji namu shi ne ya jawo mana sanadinta,

A yau sai ta koke-koke muke yi na Ƙin jinin ganinta.

 

 1. Komai yawan iya ƘoƘarinmu ba ma iya kawar da ita,

Gama ta yi zuwan shigar sojan badakkare ne abinta.

 

 1. Mai saye da sayarwa babinsa iya yake wa bauta,

Kai duk sana’a ma ana yi ne domin a kubce mata.

 

 1. A kullum tana gamawa da abin da rai yake buƘata,

Kuɗi ba a ci nai mu saya ake yi da shi idan ka fahimta.

 

 1. Komai yawan kuɗinka idan babu kwayar hatsi lallai za a yi ta.

A nan ne hankula za su tashi sai ka ji ana ta ambatarta.

 

 1. Ba yadda za mu yi mu rabu da wannan halitta,

Sai ranar da rai ya kama hanyar zuwa makwanta.

 

 1. A can makwantar ma akwai wacce ake mana batunta,

Yunwa ta lahira ce abar kowa ya ji tsoronta.

 

 1. Ta duniya layyo su nomau ma suna magance mana da ita,

Noma suke yi suna samun dammunan magance mana ita.

 

 1. Ta nan duniya su nomau ma suna magance mana da ita,

Noma suke yi suna samun dammunan magance mana ita.

 

 1. Tana da na’urori masu sa wa dammuna duk su salwanta,

Da zarar sun salwanta zuwa take yi ta yi mana lalata.

 

 1. Yara su kuka suke yi manya suna ɗan haƘureta.

Manyan ma in ta yi kamari a fuskarsu ake ganeta.

 

 1. Akwai masu ce mata yunwa shegiya ce a don tsananin zafinta,

Masu faɗin haka hala kwana suka yi suna jinta.

 

 1. A duk duniya ba halittar da bata da saninta,

Hatta har halittun da ba sa magana suna da saninta.

 

 1. Wasu “Food Hotels” nan ne sansanin mayakanta,

Komai yawan iya ƘoƘarinsu ba sa iya kawar da ita.

 

 1. Mutum da dabba ba wanda ba shi da saninta,

Jarirai su ne suka fi yawan fallasarta.

 

 1. Da ta ɗan tabe su kuka suke yi na alamin jinta,

Iyaye suka ba su mama shi ne garkuwar kareta.

 

 1. Aure yakan sukurkuce a inda ta yi ɗanɗazonta,

Mace yakan ce ba ni yarda yunwa ta ci min illata.

 

 1. Wata takan bau gyale ta nufi gidan alƘali abinta,

Da isarta za ta fara fesa masa abin da ya kawota.

 

 1. AlƘali ya kan ce kina da gaskiya ni ma na santa,

A kullum tana zuwa gidana ina ta fafararta.

 

 1. Je ki na raba aurenku a kan abin da ki ka ambata,

Karɓi takardarki Allah ya ba ki wani mai iya korarta.

 

 1. Yunwa takan sa abar gida don tsananin zafinta,

A shiga uwa duniya neman makaman yaƘarta.

 

 1. Wani a can uwa duniya zai mace ya barta,

Wani kuwa sata za ta sa shi don ya samu ya kurce mata.

 

 1. Gaya min wani mai rai da ba shi da saninta,

A nawa sanin mala’iƘu ne kaɗai ba sa jinta.

 

 1. Sauran halittu da ke a doron kasa su ma suna da saninta,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here