Jami’an Tsaron STF SUn Kama Mutane 9 Da BindIgogi A Filato

0
1142

Jami’an tsaro na musamman da ake kira STF, sun iza Ƙeyar wasu mutane tara (9) da suke tuhuma da samunsu da makamai ba bisa Ƙa’ida ba a Ƙauyen Du da yake cikin Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu da ke Jahar Filato.

Da yake nuna su ga manema labarai a hedikwatar STF, mai magana da yawun jami’an tsaron, Kyaftin Salisu Mustapha ya ce sun ci nasarar cafke waɗannan miyagun jama’a ne da misalin Ƙarfe 10.20 na daren Talatar da ta gabata bayan da jami’an suka sami karɓar wani kira na gaggawa ta hanyar lambobin tarho da jama’a suke buga masu.

Ya ce an sanar da su ne cewa, ana ta jin Ƙarar harbe-harben bindigogi a wajen garuruwan Du da Shenba da Bisichi da ke a Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.

Ya ce, “jami’anmu sun kewaye yankunan a inda suka sami cafke mutane tara a cikin motoci huɗu daban-daban da suka haɗa da Vento da take ɗauke da lamba AH 454 BLD (Filato) da Vectra mai lamba AA 87 MLF (Katsina) da Marsandi mai lamba EC 210 LND (Legas) da kuma Honda mai lamba AG 718 daga Jahar Filato.

Jami’in tsaron ya ci gaba da cewa, sun kama kayayyaki daga wurin waɗanda ake tuhuma da suka haɗa da bindigogi Ƙirar AK 47 da wata Ƙirar FN da kuma bindiga mai sarrafa kanta, SMG, haka kuma da wata guda ɗaya Ƙirar gida Ƙarama da doguwa guda ɗaya tare da wuƘa da albarusai da dama.

Ya ci gaba da bayanin cewa, sun gano cewa, waɗanda ake tuhumar sun sami waɗannan mugayen makamai ne daga wurare daban-daban a cikin jahar, inda suka fuskanci juna da waɗansu ‘yan bindiga daɗi da suka je satar shanu a Ƙauyen na Du.

Kyaftin Salisu ya ci gaba da cewa, dukkan waɗanda da ake tuhuma da kayayyakin suna tsare a hannun STF.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here