Gwamnatocin Baya ba Su yi komai Ba Kan Matsalar Fulani – Mai Kano

0
1829

Isah Ahmed Daga Jos

Shugaban sabuwar kungiyar matasan al\’ummar Fulani ta qasa  Jonde Jam Alhaji Sa\’idu Abdullahi Maikano, ya bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata ba su iya yin komai ba, wajen magance matsalolin da suke damun
al\’ummar Fulani a Nijeriya. Alhaji Sa\’idu Abdullahi Maikano ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin qaddamar da wannan sabuwar qungiya ta matasan fulani ta qasa mai suna Jonde Jam da aka gudanar a garin Jos.

Ya ce an yi shekara da shekaru a Nijeriya ana kashe fulani ana sace shanunsu amma abin takaici babu wani mataki da gwamnatocin da suka gabata suka xauka, don magance wannan matsala da take ciwa fulani tuwo a kwarya.

Alhaji Sa\’idu Maikano ya yi bayanin cewa  qungiyoyin al\’ummar fulani na  miyetti Allah da qungiyar Kautel hore basa yin abin da ya kamata na kare hakkoki da martabar  al\’ummar Fulani a Nijeriya.

Ya ce da waxannan qungiyoyi suna yin abubuwan da suka kamata na kare mutumcin al\’ummar fulani da babu yadda za a yi  matasan fulani  su fito su kafa wannan qungiya, don kare mutumcin al\’ummar Fulani.

\’\’Da qungiyoyin Fulanin nan  suna yin abin da ya kamata a Nijeriya, ya ya za a yi kan mutum xaya da aka sace a Nijeriya wanda  ba a tabbatar da ko su waye suka sace shi ba. Ace za a kori al\’ummar fulani gabaki xaya  daga yankin yarbawa.

Ya yi kira ga Shugaban qasa Muhammad Buhari kan ya duba irin  kisa da sace sacen shanun da ake yiwa al\’ummar Fulani a qasar nan. \’\’A kullum ana tare yaran fulani a kan hanyoyi  a kashe su a kwace dukiyarsu a
qasar nan. Don haka muna rokon shugaban qasa ya taimaka ya duba wannan matsala da take damun al\’ummar Fulani\’\’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here