Gobara Ta Kone Wani Gida Kurmus

0
1940

 

 

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AN samu tashin gobara da ta kone wani gida kurmus a Hayin Malam Bello da ke Rigasa Kaduna,  bangaren da abin ya shafa na iyalan Malam Muhammad Ibrahim Kazaure ne, sai dai ba a sami asarar rai ba a faruwar wannan mummunar al’amari.

Lamarin dai ya auku ne a layin Gubuci a ranar Talata da ta gabata da misalin karfe sha daya da rabi na safe, jim kadan bayan fitar mai gidan shi da iyalansa, wanda hakan ya sanya ba a san ko mene ne sila ko musabbabin tashin gobarar ba.

Wakilinmu da ya ziyarci wurin da lamarin ya auku, sa\’ilin da ma\’aikatan kashe gobara da jama\’a ke ta kokarin kawo karshen wutar, ya gano cewa babu abin da aka fitar a gidan wanda wutar ba ta kona shi ba face sai Alkur\’ani mai girma da motar mutumin da ke cikin gidan da aka yi waje da ita.

Da yake zantawa da wasu daga  makwabtan gidan, sun bayyana cewa suna ganin wannan wutar na da nasaba da karin karfin wutar lantarki da aka yi kafin dauke ta, wanda kila sun bar kayayyakin da suke amfani da lantarki a kunne.

Hakazalika, a jawabin wani jami\’in ma\’aikatar kashe gobarar da ya bukaci sakaye sunan shi, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya kara da cewa wannan gobarar ita ce ta uku a yau da aka kira su kuma suka je kashewa sakamakon canjin lokaci na hunturu da aka shiga yanzu.

A karshen, jami\’in ya jajanta wa mutanen da abin ya shafa kana ya gargadi jama\’a musamman mata, da su guji barin kayan wuta ko wutar murhu da sauran abubuwan wuta da kayan wuta ba tare da sun kashe ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here