Yan Sanda Sun Hallaka Masu Satar Shanu 3

0
2061

Rundunar yan sandan jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce jami\’anta sun hallaka wasu mutane uku da ake zargi
masu satar shanu ne, yayin musayar wutar da bangororin biyu suka yi.

Rundunar ta kuma ce an kwantar da wasu uku da suka samu raunuka yayin arangamar, sannan kuma aka kama wasu mutane 9 daban.

Kwamishinan \’yan sandan Jihar ta Kano, Muhammad Musa Katsina ne ya sheda wa ‘yan jaridu a jahar cewa sun kuma kwato daruruwan shanu gami da bindigogi a wani yunkuri na fatattakar barayin shanu da rundunar ta ce ta dukufa a kai.

Matsalar satar shanu na daga cikin matsalolin da ake fuskanta ta fanin tsaro a yankin arewa lamarin da ya janyo asarar dukiya da kuma rayuka masu yawan gaske.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here