Martani Ga Yasir Ramadan Gwale

0
2817
Daga Ibrahim Sanyi-Sanyi Taba-ka-lashe
GAJERAN martani ne na rubuto  ga rubutu ko hannun-ka-mai-sanda da Malam Yasir Ramadan Gwale, ya yi a kan yiwuwar maimaita irin abin da ya kai ga kifar da gwamnatin Mohammed Mursi ta Misra a kan sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta kasar Najeriya.
Malam Yasir kenan! Matsalolin siyasa da tattalin arziki da Nijeriya take fama da su a yanzu ko kusa ba za a hada su da wadanda Misra ta yi fama da su a lokacin mulkin Mursi/Ikhwan ba. Sannan tun da \’yan Nijeriya suka iya jure bakin zaluncin da gwamnatin Jonathan ta tsoma su ciki na rashin tsaro, cin hanci da tabarbarewar tattalin arziki, ba su yi bore ba; mene ne zai tunzura su yi wa sabuwar gwamnatin da suka yi uwa suka yi makarbiya a samar da ita, bore?
Wannan sharhi na ka da wanda Aliyu Tilde ya yi, kun yi shi ne kawai domin isar da ra\’ayinku ga masu bibiyar rubututtukan da kuke yi. Kamar yadda a can baya lokacin da ake kokarin tsayar da dan takara a jam\’iyyar adawa ta APC, kuka yi hasashen cewa muddin Arewa na son kada Jonathan a zabe, to ya zame mata tilas ta tsayar da Bayarbe Musulmi daga bangaren Kudu-maso Yammacin Nijeriya a karkashin jam\’iyyar ta adawa.
Amma da Allah ya kaddara cewa Buhari ne shugaban kasa a zaben 2015, sai ga shi ya tabbatar masa da mulki duk da irin kwarbai da daga da aka sha kamar za ai yaki. Haka nan Allah zai kare mana shi daga sharrin masharranta da makiya masu neman kifar da gwamnatinsa ta hanyar ku ko tunzura \’yan kasa su yi bore.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here