Akwai Bukatar Karin Makarantun Gwamnati A Gundumar Rigasa

1
2110

Usman Nasidi, Daga Kaduna

WATA kungiyar wayar da kai da azama, wato (Rigasa Action and Awareness  Forum RAAF) da ke gundumar Rigasa Kaduna sun koka bisa ga karancin yawan makarantu a yankin gundumar don yaransu su cimma nasarar samun ingantaccen ilimin da ake bukata a gundunar.
Mataimakin shugaban kungiyar, Malam Abdulmumin ne ya bayyana hakan a wajen wani taron kungiyar a makon da ya gabata inda ya bayyana cewa yawan yaran da suke da su ya sha karfin yawan makarantun da suke da su a gundunmar.
Abdulmumin, ya kara da cewa a sakamakon sabon shirin ba da ilimi kyauta da akeyi  a yanzu, wasu iyayen sun cire yaransu daga makarantun kudi zuwa na gwamnatin al’amarin da ya kara cinkoson ainun.
Ya ce \” yanzu haka yawan yaran ya fara haifar da wasu matsaloli irin na batar yara da sumewa a cikin azuzuwan, saboda irin yawa da cinkoson da ake fuskanta a wasu makarantun firamaren da ke garin don dama ba isassun wurin ajiye su balle a karantar da su.\”
A cewarsa, a halin yanzu an kai wani matsayi wanda wasu yaran babu inda za a sa su a cikin azuzuwan, face sai dai a bar su a cikin filin makarantun ko harabar suna zaman jiran tsammani.
Hakazalika, ya danganta matsalar batar yaran da sakaci irin na iyaye masu kai yaran da ba su da wayo ko shekarunsu bai kai na a dauke su a makarantun ba, kana su tirsasa wa hukumar makarantun don daukar yaran ko su kai su kara a gaba.
A karshe, Malam Abdulmumin ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi kokarin kara yawan makarantun a gundumar wanda akalla ko da a samu makarantun firamare 50 ne da sakandare 20.

 

1 COMMENT

  1. kamar yadda za a iya gani a wannan hoton da ke cikin wannan labarin mai girma gwamnan jahar Kaduna malam Nasiru Ahmad Ek-Rufa’i ne a cikin ofishinsa yana aiki kuma hakan ya faru ne sakamakon karatun da gwamnan ya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here