An Yaye Daliban Hadda Karo Na Farko

0
1243

Usman Nasidi, Daga Kaduna

AN gudanar da taron walimar yaye wasu daliban haddar Alkur\’ani mai girma karo na farko da masu sauka karo na goma a makarantar Islamiyyar Al- Hassan Ta\’alimid Dinil Islam, Wa tahafizul Kur\’an da ke Rigasa Kaduna.
Daliban masu haddar Alkur\’nin mai girma sun hada da yara maza su shida kana da masu saukar su sha uku wanda ya gudana a ranar Asabar, sai na matan yara masu hadda su shida da yara mata da matan aure masu sauka su arba\’in da biyu shi ma wanda ya gudana washegari a shekaranjiya Lahadi.
Babban bako mai jawabi a wajen taron kuma shugaban majalisar malamai na karamar hukumar Igabi, Sheikh Musa Muhammad ya bukaci al\’umma da su rika taimaka wa addinin Allah da dukiyoyinsu domin samun ci gaba a cikin al\’amura na yau da kullum da kuma cikin al\’umma baki daya.
Ya ce \” ya kamata mazanmu da matanmu da mu himmatu wajen taimaka wa addinin Allah da dukiyarmu, iliminmu, karfinmu da shawarwari don ganin an samu nasara a duk wani fannin da ya shafi addinin na Musulunci.\”
Ita kuwa a nata jawabin, shugabar makarantar, Malama Yahanasu Idris Mika\’il, ta gargadi iyaye mata da su kara jajircewa kuma su himmatu ta fannin da bada dukiyoyinsu wajen taimaka wa addinin Allah, don wannan aikin sadakatul jariya ce wacce za su tsinta a gaba.
A karshe, Malama Yahanasu ta yi kira ga iyayen yara da mahukunta musamman gwamnati da su rika basu haddin kai da kawo musu dauki na tallafin kayan more rayuwa da yara daliban za su kara samun saukin yin karatun cikin jin dadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here