Marubutan Arewa Su Rungumi rubuta Littattafan Da Ake Amfani Da Su A Makarantu—Ibrahim Ibzar

  0
  2215

  Isah Ahmed, Daga Jos

  MALAM Ibrahim Abdullahi Muhammad  shi ne Manajin Daraktan Kamfanin
  dabi’i da wallafa mai suna Ibzar Publishing Company  Ltd da ke garin

  Jos, babban birnin jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da
  wakilinmu ya bayyana cewa babu shakka rungumar harkar rubuta
  littattafan da ake amfani da su a makarantu zai taimaka wajen bunkasa
  tattalin arzikin arewa da kasa baki daya. Don haka ya shawarci
  marubutan arewa kan su rungumi wannan fanni musamman ganin yadda aka
  tafi aka  bar wannan yanki a baya, musamman a wannan fanni.
  Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: Wadanne dalilai ne kake ganin suka sanya aka bar yankin arewa a
  baya a wajen rubucerubucen littattafan da ake amfani da su a makarantu?

  Ibrahim Ibzar: Abin da nake ganin ya sanya aka bar yankin arewa a

  baya a fannin rubucerubacen littattafan da ake amfani da su a

  makarantun kasar nan,  na farko shi ne tsarin ita kanta Nijeriya.
  Domin ita Nijeriya abin da ya shafi harkokin ilmin zamani, wato ilmin
  boko wanda Turawa suka zo da shi, sun fara zama ne a kudancin kasar
  nan, suka fara dabba\’a wannan ilmi na boko kafin su zo nan arewa.
  Don haka aka yi mana rata kan harkokin rubucerubuce, musamman kan

  littattafan da ake amfani da su a makarantu. Marubutan kuduncin kasar

  nan sun mamaye wannan fanni.
  Duk da  muna da namu tsarin rubucerubucen kafin zuwan Turawa. Muna

  da hazikan marubuta a nan arewa, amma ba su damu da rubuta littattafan

  da ake amfani da su a makarantu sosai ba.

  Don haka a kullum nake kira ga marubutanmu na nan arewa kan su tashi
  tsaye, su shiga fannin rubuta littattafan da ake amfani da su a

  makarantun kasar nan. Tun daga makarantun firamare da sakandare har ya
  zuwa jami\’o\’i  musamman kan darussan lissafi da turanci da kimiyya da
  fasaha da adabi da zamantakewa da dai sauransu.
  Domin wannan fanni na rubucerubucen littattafan da ake amfani da su a

  makarantu, fanni ne da zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin
  yankin arewa. Domin kamar  a kowane zangon karatu, kusan kowane
  uba  yana kashe kudi ta fannin sayen littattafai ko ta hanyar biyan
  kudi a dunkule ga makarantar da yaransa suke karatu.
  Bayan haka wani dalilin  kuma da nake ganin ya sanya aka bar mu a baya,

  shi ne, muna da karancin kamfanonin buga littattafai a nan arewa. Domin

  irin wadannan kamfanoni da suke buga irin wadannan littattafai,  sun fi

  yawa ne a Legas da sauran sassan kudancin kasar nan.
  GTK: To, wadanne hanyoyi ne kake ganin za a bi a tallafa wa marubutan

  na arewa don ganin sun rungumi rubucerubucen litattafan da ake

  amfani da su a makarantu?

  Ibrahim Ibzar: A kowanne lokaci idan aka zo maganar tallafa wa masu

  rubucerubucen littattafai, nakan ce dole ne gwamnatoci da sauran masu

  hannu da shuni na arewa  su shigo wannan fanni, don su tallafa.

  Domin kamar yadda na fada muna da marubuta masu kwazo, wadanda za su

  iya rubuta dukkan littattafan da ake bukata a makarantun kasar nan.

  Amma damuwar ita ce kamfanonin da za su buga irin wadannan littattafai,

  domin ba mu da irin wadannan kamfanoni da yawa a arewa.

  Don haka dole ne gwamnatocin arewa da sauran masu hannu da shuni, su

  shigo don tallafa wa marubutan, ta hanyar kafa irin wadannan kamfanoni

  ta yadda za a sami damar buga irin wadannan littattafai, cikin sauki a

  nan arewa. Wannan ita ce babbar hanyar da za a karfafa wa marubutan

  arewa gwiwa.
  Idan aka karfafa wa marubutanmu na arewa gwiwa, babu shakka za su
  rubuta littattafan da za su taimaka wajen bunkasa kasar nan. Domin shi
  mutumin arewa mutum ne wanda yake da tsarin addini da al\’adu tun kafin
  zuwan Turawa kasar nan.

  GTK:  Yaya ka ga yadda mutanen arewa suke karatu a halin yanzu?

  Ibrahim Ibzar: A gaskiya yanzu mutanen arewa suna karatu musamman idan

  aka yi la\’akari da shekarun baya, domin a yanzu babu wani fannin da
  mutanen arewa ba sa karatu a kansa.

  GTK: To a karshe wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati da

  marubuta, musamman na yankin arewa?
  Ibrahim Ibzar:  Kirana ga gwamnati da marubuta da sauran al\’umma shi

  ne a ta shi a rungumi fannin rubucerubuce, domin wannan fanni zai

  iya canza rayuwar al\’umma, zuwa ga yadda ake son ta zama.
  Idan aka inganta littattafan da ake amfani da su a makarantu, aka koyar
  da yara yadda ya kamata,  za a sami magabata na kwarai, ta yadda  a
  gaba za a sami kyakkyawar al\’umma, wadda za ta ginu a kan akidun da aka
  gina ta.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here