‘Yan Sanda A Kano Sun Dukufa Wajen Kamo Mata 4 ‘Yan Kunar Bakin Wake

0
1678
RABO HALADU, Daga Kaduna

HUKUMOMI a jihar Kano  sun ce
mutane biyu sun kara mutuwa sakamakon
harin da aka kai a kasuwar sayar da
wayoyin hannu da ke birnin na Kano.

Jami\’an asibiti sun shaida wa wakilinmu cewa
mutanen da suka sake mutuwar na cikin
wadanda aka kai asibiti.
Mutanen sama da 50 ne suka jikkata.

Rahotannin dai sun ce wasu mata biyu \’yan
kunar bakin wake ne suka kai harin.
Wani dan kasuwar ya shaida wa wakilinmu
cewa ya hango matan sun wuce ta gaban
shagonsa, jim kadan bayan hakan kuma sai ya
ji karar fashewar bam.
Kwamishinan \’yan sandan jihar, Muhammad

Musa Katsina ya ce rundunarsa tana neman
wadansu matan hudu da su ma ake zarginsu da
hannu a wannan hari.
Bam na farko ya fashe ne a waje yayin da
dayan kuma ya fashe a cikin kasuwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here