Rikita Rikitar Albashi Gwamnatin filato Ta tsame Hannunta

0
2076

Isah Ahmed Daga Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta bayyana cewa  bata tare da bayanin da aka
yi, na  cewa gwamnonin jihohin kasar nan ba za su iya ci gaba da biyan
ma\’aikata  matsakaicin  albashi na naira dubu 18 ba.

Daraktan watsa labaran gwamnan jihar  Mista Samuel Emmanuel Nanle ne ya bayyana haka
a lokacin da yake zantawa da \’yan jarida a garin Jos.

Ya ce gwamnatin jihar Filato bata tare da wannan bayani da aka yi,
don haka  zata cigaba da biyan ma\’aikatan jihar matsakaicin albashi na
naira dubu 18.

\’\’Gwamnan jihar Filato Simon Lalong,  ya ce ba zai rage yawan
ma\’aikatan jihar  ba, Kuma ba zai rage yawan albashin ma\’aikatan jihar
ba. Babban abin da gwamnatin Filato ta sanya a gaba shi ne kokarin
samo hanyoyin samun kudaden shiga a jihar. Da zarar kudade sun shigowa
gwamnatin jihar,  zata biya ma\’aikatan jihar albashinsu nan take\’\’.

Daraktan ya yi bayanin cewa a jihar Filato duk ma\’aikaci  daya za  a
sami  mutum 8 suna jingine da shi, Don haka idan aka ce za rage
albashin ma\’aikata, ko kuma za a rage yawan ma\’aikata a jihar, za a
kara saka jama\’ar jihar a cikin wani mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here