Gwamnati ta kira kamfanoni masu zuba jari kan noma zuwa Nijeriya –Tasi\’u Bako

0
1435

Isah Ahmed Daga  Jos

Shugaban kungiyar matasa manona na arewacin Nijeriya  Alhaji Tasi\’u
Bako Nabawa Saminaka, ya yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin
shugaban qasa Muhammad Buhari,  ta kirawo kamfanoni masu zuba jari kan
harkokin noma daga kasashen duniya zuwa kasar nan, domin su zo su zuba
jari. Alhaji Tasi\’u Bako Nabawa Saminaka, ya yi wannan kiran ne a
lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce kamar yadda shugaban qasa Muhammad Buhari  yake ta zuwa kasashen
duniya don kawo masu zuba jari zuwa kasar nan, ya kamata  ya  mayar da
hankali kan kirawo masu zuba jari kan noma zuwa kasar nan.

Alhaji Tasi\’u Bako ya yi bayanin cewa yin haka ya zama wajibi, domin
manoman kasar nan suna fuskantar matsalar rashin kamfanonin da zasu
sayi kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa, da kuma kamfanonin da
zasu zuba jari kan harkokin noma a kasar nan.

\’\’A kira kamfanoni da masana\’antu masu zuba jari da masana kan noma
daga kasashen duniya zuwa Nijeriya, don su shigo harkar noma a
Nijeriya don a samu a bunkasa harkokin noma a Nijeriya, ta yadda zamu
yi kafada da kafada manyan kasashen da suke noma a duniya.\’\’

Ya ce duk yadda manomi ya kai ga iya noma, idan ya noma kaya ba masu
saye to matsala ta shiga ciki. Don haka muna kira ga gwamnatin nan,
kan ta dauki matakai na ganin an magance wannan matsala.

\’\’A shekarun baya  harkar noma ne ya bunkasa Nijeriya domin  ada noman
gyada da auduga ne hanyoyin samun kudade shiga  a Nijeriya. Amma da
man fetur yazo sai aka yi watsi da aikin noma a Nijeriya. To yanzu an
sami matsala kan harkar mai a duk duniya, sakamakon faduwar
farashinsa a kasuwar duniya. Don haka   ya zama dole gwamnatin
Nijeriya ta waiwayi harkar noma ta  bunkasa shi, don samun hanyoyin
kudaden shiga\’\’.

Ya ce yanzu mutane sun yiwa gwamnati yawa a Nijeriya, don haka ba zata
iya samarwa kowa aiki ba, dole ne sai dai  mu rungumi aikin noma domin
shi ne zai baiwa kowa aiki a Nijeriya.

Ya ce yanzu a kullum ana dada bunkasa aikin noma  a duniya,   ana fito
da sababbin dabarun noma. Don haka ya zama wajibi muma  a Nijeriya mu
jiyo mu rungumi harkokin noma mu bunqasa shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here