Wani Boka Ya sanya Matasa Sun Yi Fawar Abokinsu

0
2050

Usman Nasidi Daga Kaduna

Al’ummar Unguwar Zubairu da ke Mangwaro- Biyu a karamar Hukumar Giwa a
Jihar Kaduna sun wayi gari cikin firgici da dimauta bayan da suka iske
gawar wani dansu mai suna Zubairu Abubakar mai shekara 22, an yi masa
yankan rago tare da yin fawan gawarsa.

Wakilinmu daya ziyarci kauyen domin tantance yadda lamarin ya wakana
wajen mahaifin marigayin, Liman Abubakar Zubairu wanda ke jinyar
karaya sanadiyyar rusawar gini a kansa ya shaida cewa, a ranar Talata
bayan Magariba suna tare da marigayin sai aka kira shi ta bayan gida
sai ya nemi yardasa har ya
karbi aron tocilarsa ya fita.

Yace \” to daga nan bai dawo ba har karfe 12:00 na dare, sai hankalinmu
ya tashi ganin bai taba kai haka ba,
kuma kusan shi yake kula da ni don shi ne babban dana, saboda haka
muka kwana ba mu iya barci ba don tunanin halin da yake ciki.”

Mahaifin ya kara da cewa da gari ya waye dan wansa zai shiga gona da
misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Larabar makon jiya, sai kawai ya
ga gawar shi cikin wani hali ya rugo a guje ya fada wa ’yan uwa sai
aka dunguma zuwa wurin aka dauko
gawar, amma da Jin yadda aka yi masa sai yace a wuce da shi can gidan yayansa.

Mahaifiyar marigayin Malama Raliya cikin kuka ta bayyana wa wakilinmu
cewa, “marigayin ne ma ya yanka mata kubewar da na yi miya da ita a
ranar.

Acewarta, ya ce \” mama ina jin yunwa in kin gama tuwon ki sa min da
yawa sannan ya tambaye ni in ba shi Naira goma, sai na kawo Naira
ashirin na ba shi rabuwana da shi ke nan sai na ji wannan mugun labari
a kansa,” inji ta.\”

Mai unguwar garin Malam Umaru Musa wanda da shi ne aka dauko gawar
marigayin da aka yi masa wanka ya ce “Yadda na ga gawar ba ta da kyan
gani domin yankar rago suka yi masa kuma suka cire makogoronsa da
harshensa da kuma agaran kafafunsa, suka kuma zare
jijiyoyin hannayensa biyu, tare da yanke farjinsa.

Ya kara da cewa wannan ne halin da muka samu marigayi Zubairu, kuma
bayan sun dawo, sai suka jawo hankalin al’ummar unguwar da su kwantar
da hankulansu, kana ya sanar da hakiminsa tare da jami’an ’yan sanda,
wanda nan take suka zo
suka duba gawar kuma suka yi abin da duk ya kamata kamin su ba da
umarni a yi masa sutura.

Yace \” daga nan sai muka dauki matakin kula da yanayin zirga-zirgar
jama’armu cikin, kuma cikin ikon Allah
da daddare sai muka gano daya daga cikin yaran kuma makkwabcin gidan
su, mai suna Abubakar Iliyasu da wani irin kamanni da ba mu gane ba,
nan fa muka fara bincikensa, muka ga wasu abubuwa na ban mamaki a
wajensa.\”

Acewarsa, kayan da suke jikinsa a lokacin da suka yi wannan aika-aika
duk sun baci da jinni, inda ya bayyana cewa wani boka ne ya sanya su
kawo masa sassan jikin mutum zai basu
Naira 150, inda ya fada masu cewa daya daga cikin abokan aikinsa mai
suna Yusuf Ibrahim wanda aka fi sani da Battu Bafulatani da rugarsu ke
nan kusa da su na daya daga ciki, inda shi ma suka je  suka samu
kayayyakin da suka kashe marigayi da shi, sai suka muka mika su ga
’yan sanda.

Binciken da wakilinmu ya yi ya gano cewa bokan da ya sa matasan suka
kashe abokinsu ya gudu daga garin bayan da ya ji an kama yaran.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan Mai kula da Shiyya ta daya da ke
Zariya, Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya
ce sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a wannan danyen aikin
kuma sun baza komarsu domin kamo wanda ake zargi da sanyawa ayi kisan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here