Ban Aiki Kowa Ya Tayar Da Fitina Ba – David Mark

  0
  1562

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  Tsohon shugaban majalisar dattijai
  David Mark ya bukaci jama\’ar
  mazabarsa da kada su tayar da fitina
  sakamakon soke zabensa da wata kotu ta yi.
  A cikin wata sanarwa, Sanata Mark ya bukaci
  jama\’ar mazabar sa da kada su karaya, a
  maimakon haka, su kara shiri na tunkarar
  zaben da za a sake gudanarwa.
  Ya ce yana da yakinin zai sake lashe zaben idan
  aka sake gudanar da shi.
  Wata kotun daukaka kara ce da ke zama a
  Makurdi babban birnin jihar Benue ta soke
  zaben da aka yiwa Sanata David Mark.
  Kotun ta ce akwai kuskure a matsayin da
  hukumar zabe ta kasar INEC ta dauka na
  baiyana David Mark, dan takarar Jam\’iyyar PDP
  a matsayin wanda ya lashe zaben yan majalisar
  dattijai a shiyyar kudancin Benue wanda aka
  gudanar a ranar 28 ga watan Maris
  Dan takarar sanata a karkashin jam\’iyyar APC
  shiyyar kudancin Benue Donald Onjeh shi ne ya
  shigar da karar.
  Kotun ta bayar da umarnin a sake zaben
  kujerar majalisar dattijan cikin kwanaki casa\’in.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here