\’An kashe \’yan Boko Haram 100 a Kamaru\’

0
1481

Daga Usman Nasidi

Sojojin Jamhuriyar Kamaru sun ce sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 100 a wani samame da suka kai musu.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato wasu jami\’an gwamnatin kasar na cewa an ceto mutane 900 da \’yan Boko Haram din suka yi garkuwa da su.

Hakan na faru ne a daidai lokacin da wasu \’yan bindiga biyu sun kai hari a arewacin kasar a daren ranar Talata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla uku.

Kazalika an kai makamancin wannan harin a garin Waza da ke da yankin
arewa mai nisa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida —
ciki har da maharan guda uku.

Jami\’an tsaro sun kashe \’yar kunar bakin wake ta uku a yayin da take
kokarin tayar da bam din da ke jikinta.

Kasar Kamaru dai na yawan fuskantar hare- haren mayakan kungiyar Boko
Haram saboda
shiga cikin kasashen da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da \’yan Boko Haram.

Sauran kasashen da suke taimakawa Najeriyar su ne Chadi da Nijar da kuma Benin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here