EFCC ta kama Bafarawa da Shugaban AIT

0
2093

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta\’annati, EFCC, ta kame tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, da kuma shugaban gidan talabijin na AIT a kasar Nigeria, Raymond Dokpesi.

Wata majiya a hukumar ta EFCC ta tabbatar wa da yan jaridu cewa, kama Bafarawa da Dokpesi na da alaka da binciken da ake yi a kasar game da badakalar dala biliyan biyu da ake zargin an yi sama da fadi da su a ofishin tsohon mai bai wa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.

Wani kwamiti da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa don bincika kudaden da aka kashe kan samar da makamai don yaki da Boko Haram a Nigeria ya ce, ya gano an yi sama da fadi da kudaden da suka zarta dala biliyan biyu.

 

\"Dokpesi\"

A don haka ne hukumar ta EFCC ke ci gaba da kama wadanda ake zargi da hannu a badakalar, wadanda suka hada da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki, da tsohon ministan kudi Bashir Yuguda, da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here