Wani Matashi Ya kashe Abokinsa Da Tsitaka

0
1436

Daga Usman Nasidi

Ana zargin wani matashi mai suna Aminu Umar mai shekaru 19 da kisan abokinsa mai suna Shafi’u Muhammad dan shekaru 18 da haihuwa, inda ya yi amfani da wani abu mai kaifi ya caka masa shi a wuya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Rahotanni sun bayyana cewa matasan biyu, wadanda dukkaninsu ’yan asalin karamar Hukumar garin Isa ne cikin Jihar Sakkwato kuma abokan juna ne da suke zaune a Wapa a karamar Hukumar Fagge, Jihar Kano.

Binciken ya nuna cewa wata jayyaya ce ta shiga tsakanin abokan biyu, inda a karshe Aminu Umar, ya fusata ya dauko wani makami mai kaifi (tsitaka), ya caka wa Shafi’u, a makogwaro.

lamarin da ya jawo ya fadi yana zubar da jini, wanda ganin abin da ya faru da Shafi\’u,sai wanda ake
zargin Aminu ya cika wandonsa da iska.

Wani ganau wanda ya nemi a sakaya  sunansa ya shaida wa manema labarai
cewa lokacin da jama’ar
suka ga haka sai suka dauke shi zuwa asibiti, inda aka tababtar da rasuwarsa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya
bayyana cewa zuwa yanzu jami’ansu sun cafke sauran abokan zaman
mutanen a lokacin da suke kan hanyarsu ta guduwa daga Kano,kuma ana gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here