Duk mai haddar Al\’kura\’ani babban mutum ne—Sheikh Jingir

0
3525

Isah Ahmed Daga  Jos

Shugaban majalisar malamai   na  qungiyar Jama\’atu Izalatil Bid\’ah
Wa\’iqamatis Sunnah ta qasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir,  ya
bayyana cewa duk mai haddar Al\’qura\’ani babban mutum ne.
Sheikh Muhammad Sani Yahya  Jingir, ya bayyana haka ne a lokacin da
yake jawabi ga tawagar  \’yan takarar da suka halarci gasar karatun
Alqura\’ani ta kasa ta kungiyar daga jihar Filato tare da mika makullin
motar da aka baiwa garzon shekara na gasar Malam Abdullahi Muhammad
Abdullahi, a wajen wani taro da reshen kungiyar na jihar Filato ya
shirya a garin Jos.

Sheikh Jingir wanda mataimakin shugaban majalisar malamai na kasa na
biyu kuma Sa\’i na kasa na kungiyar Sheikh Sa\’idu Hassan Jingir ya
wakilta, ya ce mai haddar Al\’qura\’ani babban mutum ne domin Manzon
Allah SAW ya ce wanda duk ya haddace Alkura\’ani kuma ya yi aiki da
shi,  a ranar tashin alkiyama zai ceci dangin uwa mutum dubu 70, kuma
zai ceci dangin uba mutum dubu 70.

Ya ce amma fa kada kuyi alfari da ilmi domin ilmi wata siffa ce ta
Allah, don haka ku rike gaskiya da amana ku yiwa malamanku addu\’a kuma
ku girmama iyayenku.

A nasa jawabin shugaban majalisar malamai na kungiyar reshen jihar
Filato Dakta Hassan Abubakar Dikko ya bayyana cewa a  duk shekara idan
aka gudanar da gasar karatun Alkura\’ani ta kasa,   mu kan zo da \’yan
takarar da suka halarci gasar tare da  kyaututtukan da suka  samo mu
gatarwa shugaban majalisar malamai Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir
don ya mikawa \’yan takarar  kyaututtukan tare da yi masu jawabi. Ya ce
don haka a bana ma muka zo da \’yan takararmu da suka halarci wannan
gasa ta kasa da aka gudanar a garin Bauchi tare da wanda ya lashe
garzon shekara na bana Malam Abdullahi Muhammad Abdullahi wanda ya
fito daga karamar hukumar Shendam ta jihar Filato. Don Malam ya mika
masa kyautar mota da kujerar makka da aka bashi a wajen gasar.

Ya ce  a bana bayan mun mika wadannan kyaututtuka da \’yan takararmu
suka samo a wannan gasa, zamu sake  shirya wata rana ta musamman wadda
zamu roki mai girma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong domin mu kai
masa waxannan \’yan takara na jiharsa da wanda yazo gwarzon shekara  a
bana, dan qaramar hukumarsa ta Shendam don ya mika masu kyaututtukan
da suka samo tare da yi masu jawabi. Ya ce wannan wani sabon salon ne
da bamu tava yin irinsa ba, a  jiha ta Filato saboda gwamnan da muke
da shi a jihar Filato a yanzu  gwamna ne na kowa da kowa a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here