Jami\’an tsaro sun kwato Shanu 250 daga Barayin Shanu a Karamar hukumar Lere

0
2580

Isah  Ahmed Daga  Jos

Jami\’an tsaron hadin gwiwar  \’yan sanda da \’yan qungiyar sintiri na
karamar hukumar Lere da
ke jihar Kaduna sun sami nasarar kwato shanu 250 daga  hanun wasu
barayin shanu a kauyen Jama\’ar Iya da  kauyen Marmara  dake yankin.

Jami\’an \’yan sandan da \’yan sintirin sun sami wannan nasara ne, a
karshen makon da ya gabata bayan da suka yi musayan harbe harbe da
barayin,  suka ci qarfinsu daga nan barayin suka zubar da
kayayyakinsu, suka gudu suka bar wadannan shanu da suka sato.

Da yake yiwa wakilinmu  bayani kan yadda wannan al\’amari ya faru,
kwamandan kungiyar \’yan sintiri na karamar hukumar Lere Malam Zubairu
Mustafa ya bayyana cewa  sakamakon fasa sansanonin barayin shanu da
sojoji da sauran jami\’an tsaro suka  yi a dajin Falgore. Don haka
wadannan barayin shanu   suka biyo ta wannan yanki, suna son su gudu.

Ya ce  irin fulanin da aka sacewa shanu a dajin na Falgore ne, suka zo
suka kawo mana rahoto mu kuma muka  tara a inda wadannan barayi suke
wucewa a kauyen  Jama\’ar Iya.

\’\’Muka tafi a mota guda da \’yan sanda da \’yan sintiri don mu kama su.
Kafin mu isa wajensu   sai aka sami wasu bata gari suka sanar dasu
cewa gamu nan tafe. Da suka ji haka sai suka shirya kayansu suka kama
hanya zasu gudu, da muka iso sai suka bude mana wuta. Muma muka mayar
da martani muka yi ta  harbe harbe da su har na tsawon kamar minti 30.
Da suka ga bamu dama, sai  suka zubar da kayayyakinsu suka shiga
gonakin rake suka gudu, suka bar shanun da suka sato. Muka tattaro
wadannan shanu muka kawo su nan babban ofishin \’yan sanda na garin
Saminaka\’\’.

Ya ce bayan haka mun sake kama wasu shanun a nan kauyen Marmara dake
wannan karamar hukuma, bayan da varayin suka guda suka bar shanun a
wajen, suma mun taho da shanun da tumakin da suka gudu suka bari.

Kwamandan ya yi bayani cewa abin da yasa wadannan varayi suka gangaro
wannan yanki, shi ne saboda baza jami\’an tsaron da gwamnati tayi  a
jihohin Zamfara da Katsina da Neja da Kaduna da Kano da Bauchi da dai
sauran wurare. Don haka suka gangaro wannan yanki suna koqarin gudu,
muna  mun tare kan iyakokinmu don kada waxannan vata garin  su shigo
mana.

Ya yi  kira ga fulani makiyaya kan duk wani  bafulatanin da zai tashi,
to yaje gidan sarkin yankin da yake ya sanar a bashi takarda ya rike
zuwa wurin da zai tafi. Idan yaje ya gabatarwa da sarkin yankin da zai
je, yin haka zai yi maganin irin wadannan vata gari.

Shi ma a zantawarsa da wakilinmu kan wannan al\’amari shugaban kungiyar
fulani makiyaya ta miyetti Allah reshen karamar hukumar Lere Alhaji
Abubakar Abdullahi [Dambarde]  ya bayyana cewa wadannan shanu da aka
kwato sun kai 250. Kuma an kawo su babban ofishin \’yan sanda ga garin
Saminaka.

Ya ce a halin yanzu fulanin da aka sacewa shanun suna ta zuwa suna
dubawa, \’\’duk wanda yazo ya duba  idan  ga shanunsu yazo da arxonsa
kuma muka  tabbatar nasa ne muna  bashi shanunsa ya tafi abinsa\’\’.

Shugaban miyetti Allah ya yi bayanin cewa  barayin shanun da suke sace
sacen shanu a jihohin Zamfara da Katsina da Neja da hukumomin tsaro
suka sanya su a gaba ne  suka dawo yankin Falgore dake jihar Kano.
\’\’Duk inda suka sami rigar Fulani sai su farwa fulani su kwashe
dabbobinsu, su yi gaba. Abin da ya kawo wadannan sace sacen dabbobi da
ake yi shi ne lalacewar matasan fulani. Domin babu wanda zai iya shiga
daji ya kai hari ya sace dabbobin bafulatani idan ba dan\’uwansa ba\’\’.

Ya yi kira ga fulani a duk inda suka ga bakin fulani da dabbobi
wadanda basu yarda dasu ba, suyi qoqari su sanar da hukuma.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin babban kakakin rundunar \’yan sanda
ta jihar Kaduna DSP Zubairu Abubakar kan wannan al\’amari, amma bai
same shi ba a waya. Amma wata majiya a ofinshin  \’yan sandan   Saminaka ta
tabbatar da cewa, tuni sun turawa rundunar \’yan sandan   jihar Kaduna
rahoton wannan al\’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here