Yan Shi\’a: Ba mu san inda El-Zakzaky yake ba

0
2040

Daga Usman Nasidi

Kungiyar Islamic movement ta \’yan Shi\’a a
Kasar Najeriya ta ce kawo yanzu ba ta san inda
shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky
yake ba.

Hakan dai ya biyo bayan samamen da sojoji
suka kai ne a gidansa da ke Gyallesu a Zariya
da kuma wasu wuraren ibada na \’yan shi\’a da
ke birnin.

Sanarwar kungiyar dake dauke da sa hannun,
Ibrahim Musa ta ce ba su san inda El-Zakzaky
yake ba ko kuma halin da yake ciki ba amma
dakarun kasar Najeriya sun kama shi a ranar Litinin da safe.

Wata diyar Sheikh Ibrahim Al Zakzaky, mai
suna Suhaila ta shaida wa manema labarai  cewa ba ta da masaniya game da inda aka tafi da mahaifinta.

Tuni dai \’yan Shi\’a din suka ce an kashe Malam
Muhammadu Turi da matar El-Zakzaky, Malama
Zeenatu da dansa, Sayyid Ali.

\’Yan shi\’ar sun kuma ce, an kashe da dama
daga cikin mabiya mazhabar ta Shi\’a, sannan
aka rusa gidan jagoran nasu.

Dukda yake, Sojojin kasar Najeriyan sun zargi kungiyar ta Shi\’a da yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar lokacin da yaje Zaria ranar Asabar, sai dai kungiyar ta musanta wannan zargi.

A cikin wata sanarwa da Kanar Sani Usman
Kukasheka ya fitar, rundunar sojin ta tabbatar
da asarar rayuka, amma ba ta yi karin bayani
ba ko mutane nawa ne suka mutu, ko kuma
daga wanne bangare.

Sanarwar ta kuma ce, da zarar an maido da
doka da oda a garin Zaria, \’yan sanda za su
gudanar da bincike domin gano abinda ya faru.

Ana dai ci gaba da zaman dar dar a Zaria,
sakamakon arangama tsakanin Sojojin da kuma
yan kungiyar ta Shia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here