Buhari Ya Bukaci Yan Najeriya Suyi Hakuri

0
1540

Rabo Haladu Daga Kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya
bai wa \’yan Najeriya  hakuri saboda
matsananciyar matsalar man fetur din da
suke fama da ita.
Shugaba Buhari ya nemi gafara ne a lokacin da
yake gabatar da kudurin kasafin kudin shekara
ta 2016 a gaban majalisar dokokin kasa.
Shugaban na Najeriya ya ce ya bayar da umarni
ga hukumar da ke kayyade farashin man fetur
da ta sake duba yadda take kayyade farashin
man, yana mai umartar ta da ta tabbatar a
yanzu farashin bai wuce N87 kan kowacce lita
daya ba.
Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin ne
na Naira tiriliyan 6.08 a kan kowacce gangar
danyen man fetur $38 da kuma N190 kan
kowacce dalar Amurka.
Haka kuma shugaba Buhari ya ce za a ware
kashi talatin cikin dari na kasafin kudin domin
gudanar da manyan ayyuka, sannan aka ware
kashi 70 cikin dari domin yin ayyukan yau-da-
kullum.
A bangaren manyan ayyuka, an ware wa
ma\’aikatar ayyuka da makamashi da kuma
gidaje N433.4 bn; yayin da ma\’aikatar sufuri ta
samu N202.0 bn; inda ayyuka na musamman
suka samu N200.0 bn.
An ware N396bn domin bai wa fannin ilimi,
yayin da aka ware N296bn kan kiwon lafiya,
sannan aka ware N294bn ga fannin samar da
tsaro a kasafin ayyukan yau-da-kullum.
Shugaban kasa ya sha alwashin
kwato dukkan kudaden kasar da aka sace, ko
da kuwa hakan zai kai shi har karshen wa\’adin
mulkinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here