Gobara ta kashe mutane da dama a kasar Najeriya 

0
1628

Daga Usman Nasidi

A Najeriya, rahotanni daga jihar Anambra na cewa kimanin mutane dari ne suka mutu a wata gobara a masana\’antar iskar gas a garin Nnewi.

Hukumomin \’yan sanda wadanda suka tabbatar
da aukuwar gobarar, ba su yi karin haske base
dangane da adadin mutanen da suka kone.

Rahotannin sun nuna cewa gobarar ta tashi ne
lokacin da wata motar dakon iskar gas ke
sauke kayan data dauko a tashar iskar gas din.

Jami\’an kashe gobara da mutanen gari sun shafe sa\’o\’i da dama kafin su kashe wutar.

Rahotannin sun ce gobarar ta ritsa ma\’aikata da yawa na kamfanin, sannan kuma ta shafi wasu gidaje da ke kusa da kamfanin.

Hakazalika a jihar kano, Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rasuwar dalibai mata su bakwai sakamakon gobarar da ta tashi a wata makarantar sakandare ta mata da ke Jogana.

Gobarar ta tashi ne a ranar Lahadi da daddare
a dakin kwannan daliban, lamarin da ya janyo
jikkatar wasu mata su 25.

Galibin daliban sun rasu ne sakamakon kokarin
ficewa daga kofofi biyu na dakin kwannan
daliban da suka kai su 500.

Gwamnatin jihar ta Kano ta bada umurnin rufe
makarantar sannan ta ce za a gudanar da
binciken musababbin afkuwar gobarar.

Gobarar ta lalata daukacin dakin kwanann
daliban sannan izuwa yanzu ana ci gaba da
ganin hayaki \’yan kwana-kwana sun shafe sa\’o\’i kafin sun kashe gobarar.

A Jahar legas kuwa, Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta tabbatar da afkuwar gobara a tsohuwar hedikwatar hukumar sadarwa ta kasa NITEL, da ke Jahar Legas.

Mai magana da yawun hukumar reshen kudu
maso yammacin Najeriya Ibrahim Farinloye ya
shaida wa manema labarai cewa, ba za a iya saurin fadar ko akwai asarar rayuka ko ta dukiyoyi ba.
Sai dai bincike ya nuna cewa hukumar kare hakkin masu ajiya a bankuna NDIC, ta koma ginin na NITEL, bayan da ofishin hukumar NDIC din ya yi gobara watanni kadan da suka gabata.

Hukumar NITEL dai ta dade da durkushewa a
Najeriya, abin da ake ta\’allakawa ga zuwan
wayar tafi da gidanka wato GSM, a shekara ta
2001.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here