Bam A Adamawa: Ya hallaka mutane 24 a kasuwar Madagali

0
1598

Daga Usman Nasidi

Rahotanni daga Madagali a jihar Adamawa
na cewar wasu \’yan kunar bakin wake sun
tayar da bam a cikin kasuwar garin.

Wani dan kasuwa ya shaida wa manema labarai cewa bam din \’daya ya tashi ne a mahautar kasuwar garin, yayin da \’dayan ya tashi a wurin da ake sayar da hatsi.

Dan Kasuwar, Ya kara da cewa ya ga gawarwakin mutane sama da ashirin da biyar wanda suka mutu a wannan harin \’yan kunar bakin waken daya gidana.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan irin
barnar da hare-haren suka haddasa a kasuwar,
amma dai hukumomi sun rufe kasuwar.

Hare-haren kunar bakin wake su ne salon da
\’yan Boko Haram ke amfani da su, tun bayan
da sojojin kasar Najeriya suka kwace iko da wasu  garuruwan da a baya ke karkashin ikon
mayakan kungiyar.

Wannan harin na zuwa ne bayan da Sojojin
Najeriya ke ikirarin karya-lagon kungiyar Boko
Haram.

Wasu bayanai sun ce mayakan Boko Haram da
dama suna nan boye a tsaunukan da ke iyakar
Najeriyar da kasar Kamaru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here