Ba a hana sanya hijabi ba – Buhari

0
1246

Daga Usman Nasidi

Fadar shugaban kasar Najeriya, ta yi watsi da jita- jitar da a ke yadawa na cewa gwamnatin kasar ta haramta sanya hijabi, wanda ta ce shi ne alamar kamalar mace musulma.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar bayan
wata hira ta musamman da shugaba Buhari ya
yi a gidan talabijan na kasar ranar Laraba,
mataimakin shugaban na musamman kan harkokin watsa labarai Mallam Garba Shehu, ya ce rade-radin ba shi da makama.

Jami\’in ya kara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da daukaka mutunci da hakkin mata musulmai a kasar, sannan kuma ya ce kowa yana da damar bin addinin da ya ke so.

Duk da cewa mataimakin ya bayyana cewa \’yan
ta\’adda na amfani da hijabi wajen aiwatar da
munanan ayyuka kan mutanen da ba su ji ba
ba su gani ba, ya ce gwamnati ba za ta dauki
wani tsattsauran mataki ba, ba tare da shawara
ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here