Kudurin gwamnatin na daukar malamai 500,000 zai bunkasa ilmi -Yahaya

0
1691

Isah Ahmed Daga Jos

Shugaban hadadiyar kungiyar makarantun islamiyya ta jihar Filato
[Ittidahu Anwaril Hidayat] Alhaji Yusuf Yahaya bayyana cewa babu
shakka bayanin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi, lokacin da ya
gabatar da kasafin kudin wannan sabuwar shekara mai zuwa. Na cewa
gwamnatin tarayya zata dauki malaman makarantu harKudurin gwamnatin Buhari na daukar malamai 500,000 zai bunkasa ilmi a
Nijeriya–Yusuf Yahaya

Isah Ahmed Daga Jos

Shugaban hadadiyar kungiyar makarantun islamiyya ta jihar Filato
[Ittidahu Anwaril Hidayat] Alhaji Yusuf Yahaya bayyana cewa babu
shakka bayanin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi, lokacin da ya
gabatar da kasafin kudin wannan sabuwar shekara mai zuwa. Na cewa
gwamnatin tarayya zata dauki malaman makarantu har mutum 500,000 zai
bunkasa harkokin ilmi a kasar nan. Alhaji Yusuf Yahaya ya bayyana haka
ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce babu shakka wannan kuduri na daukar malaman makarantun
500,000,00 da shugaban kasa ya ce za a yi, abu ne mai kyau musamman
idan aka yi la\’akari da karancin malaman makarantu da ake fama da shi
a makarantun kasar nan.

Ya yi kira ga gwamnati kan idan an tashi daukar wadannan malamai a
kula da bangare malaman makarantun islamiyya. Ya ce muna son gwamnati
ta sani, Akwai yara da yawa wadanda basa zuwa makarantun boko, amma
suna zuwa makarantun islamiyya. Kuma makarantun islamiyya nan an
inganta su a wasu jihohin kasar nan. Don lallai akwai bukatar gwamnati
ta sanya malaman makarantun islamiyya a wannan shiri.

Alhaji Yusuf Yahaya ya yi bayanin cewa kungiyar su tana goyan baya
matakin da gwamnonin arewacin kasar nan suka dauka, na cewa daga yanzu
dole sai kowace kungiyar addini ta sami izini kafin ta gudanar da
dukkan wani taro, tare da hana tare hanyoyi a duk lokacin da wata
kungiyar addini take gudanar da harkokinta.

\’\’Mun san gwamnonin arewa da manyan sarakunan arewa ba zasu yi abin da
zai cuci addinin musulunci ba, kuma mun san ba za suyi abin da zai
cuci al\’umma ba, don haka muna goyan bayan wannan mataki da suka
dauka. In kana dan kasa dole ne kabi umarnin gwamnati, matukar bai
sabawa addininka ba. Kuma gwamnatin Nijeriya tana baiwa kowa hakkin
yin addininsa musulmi da kirista. Don haka wajibi ne kowanne dan
Nijeriya ya yiwa gwamnati biyayya\’\’.

Alhaji Yusuf Yahaya ya yi kira ga al\’ummar Nijeriya su cigaba da yiwa
gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari addu\’a. Ya ce wannan gwamnati
ta shugaban kasa Muhammad Buhari gwamnati ce da take da alkibla don
haka mu cigaba da yi mata addu\’a tare da yi mata fatan alheri. mutum 500,000 zai

haka mu cigaba da yi mata addu\’a tare da yi mata fatan alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here