Wani matashi ya mutu wajen satar

0
1238

Usman Nasidi Daga Kaduna

Ranar Lahadin da ta gabata ne wani matashi da
ba a san kowane ne ba ya rasa ransa garin satar
wayar wutar lantarki a Unguwar Rimi da ke
garin Kaduna. Wannan lamari ya auku ne a titin Accra Crescent kusa da makarantar firamaren gwamnati da ke unguwar.

Dan Iyan Unguwar Rimi, Alhaji Muhammad Gidado wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ’yan sanda ne suka cire gawar mutumin daga wajen da abin ya faru.

A cewarsa, babu wanda ya san wanda ake zargi a yayin da ya yi kira ga hukumomin tsaro su kara kaimi wajen sintiri a unguwar, kasancewar mazauna unguwar sun dade ana cutar da su ta hanyar sace musu wayoyin wutar lantarki.

Dukda yake bincikin ya nuna cewa mutumin da ya
rasun, ya yi kokarin sace wayar lantarkin ne mai tsawon milimita 150 da ke babban sashin raba wuta da ke a kan titin Accra Crescent, kafin dubunsa ta cika.

Shugaban sashen ba da bayanai na kanfanin
wutar lantarki na Kaduna, Abdul’azeez Abdullahi, ya yi kira ga jama’a da abokan huldarsu su ci gaba da sanya ido tare da sanar da jami’an tsaro duk wasu take-taken mutanen da ba su amince da su ba, musamman da daddare.

A cewarsa, ayyukan irin wadannan miyagun mutane na janyo asara mai yawa ga kamfanin na wutar lantarki, wanda kuma hakan ke kara janyo rashin samun isasshiyar wutar lantarki ga jama’a.

Ya kuma gargadi miyagun mutane da su kaurace wa satar kayan wutar lantarkin domin tserar da rayukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here