An kwato kwayoyi na Naira biliyan daya a Kano Daga Usman Nasidi

0
1398

Rundunar \’yan sanda a jihar Kano ta ce ta kwato miyagun kwayoyi da suka kai Naira biliyan daya da miliyan dari 200 a cikin watanni biyu da suka wuce.

Rundunar ta ce ta kuma yi nasarar damke dillalan kwayoyi ciki har da masu dilar hodar ibilis.

Hakan na zuwa ne bayan da aka zargi jami\’an tsaro a jihar da hada baki da masu ta\’ammali da miyagun kwayoyi, zargin da suka musanta.

Kwamishinan \’yan sanda na jihar ta Kano Muhammad Musa Katsina ya ce matakin babbar nasara ce a yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar.

Bayanai sun ce galibin wadanda aka kama bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi, ba \’yan asalin jihar Kano bane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here