An kashe yan boko haram 67 a borno

0
1322

An kashe \’yan Boko Haram 67 a Borno

Daga Usman Nasidi

Rundunar sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram wacce ake kira \’Operation Lafiya Dole\’, tayi ikirarin kashe mayakan Boko HaHarlanram kusan 67 a cikin wannan makon.

Cikin wata sanarwa da mataimakin kwamandan rundunar, Manjo Janar Lucky Irabor ya fitar ta ce a kokarinsu na murkushe \’yan Boko Haram sun samu nasarar kakkabe su daga wasu sansanoni da kuma dakile wasu hare-haren \’yan kunar bakin wake.

Sanarwar ta ce \”A kan hanyar Marte, mun kashe \’yan ta\’adda 21, an raunata sojoji uku sannan mun kwace makamai masu yawa.\”

\”Dakarunmu sun fafata a Kudiye da Mijigete sun kubutar da mutane 370 sannan suka kwace makamai sannan muka kashe \’yan ta\’adda 20,\” in ji Irabor.

Manjo Janar Irabor ya kara da cewa dakarun Najeriya sun shiga kauyukan Wala da Tirkopytir da kuma Durubajuwe, inda suka yi arangama da mayakan Boko Haram sannan suka kwace makamai masu yawa.

Sanarwar ta ce sojojin sun samu wadannan nasarorin ne a daga ranar 18 zuwa 21 a watan Janairun nan ta 2016.

Daga karshe, kwamandan rundunar ta \’Operation Lafiya Dole\’, Manjo Janar Hassan Umaru ya bukaci jama\’a su ci gaba da taka tsantsan domin kubuta daga tarkon Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here