CBN zai fara cire Naira 50 a asusun ajiyar mutane

0
1429

CBN zai fara cire Naira 50 a asusun
ajiyar mutane

Daga Usman Nasidi

Babban bankin Najeriya, CBN ya ce daga yanzu za a dinga cire Naira hamsin a cikin asusun ajiyar mutane a kasar da zarar sun cire ko kuma sun ajiye kudi fiye da Naira dubu daya a cikin asusun ajiyarsu.

Wata sanarwa da babban bankin ya fitar, ta ce matakin na daga cikin yunkurin gwamnati na kara samun kudaden shiga da kuma fadada hanyoyin haraji.

CBN ya ce wannan sabon cajin da mutane za su dinga biya, mai asusun ajiyar kudi ne kawai zai biya.

Sanarwar ta ce ba za a cire kudin harajin ba daga cikin musayar kudi da mutum ya yi a cikin asusun ajiyarsa ko a banki daya ko kuma a tsakanin bankuna.

Sabon harajin na Naira hamsin wanda ake kira \’Stamp Duty\’ na daga cikin hanyoyin gwamnati na samun kudaden haraji ba ta hanyar kudin man fetur ba.

Tun bayan farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya, shugaba Muhammadu Buhari ya dauki alkawarin fadada hanyoyin samun haraji na gwamnati domin bunkasa ayyukan ci gaba a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here