\’Yan sanda za su koma kauyukan Borno

0
998

Daga Usman Nasidi

Rundunar \’yan sandan Najeriya ta ce nan gaba kadan za ta koma tafiyar da harkokin tsaro a garuruwa da kauyukan da aka kwato daga hannun \’yan Boko Haram.

Tabarbarewar tsaro a yankin ya tilasta wa hukumomin kasar mika ragamar tafiyar da harkokin tsaro a yankunan da \’yan Boko  Haram ke kaddamar da hare-here ga rundunar soji.

Rundunar \’yan sandan ta kuma ce ta tura wata tawaga domin ziyarar gani da ido kan abubuwan da ake bukata don shirya karbar ragamar harkokin tsaron yankunan.

Rundunar \’yan sandan ta ce tunda an fara samun saukin matsalolin tsaro a arewa maso gabashin kasar, musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, ta ke shirin sake aikewa da jami\’anta domin tabbatar da tsaro.

Mai magana da yawun rundunar, Olabisi Kolawole, ta ce \”Gwamnati na sane sarai cewar an lalata kusan dukkanin ofishoshin jami\’an \’yan sandan da wuraren kwanansu da ke yakin, kuma ana daukar matakai daki-daki domin ganin an sake gina wadannan wuraren.\”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here