Matsafa Sun Kwakulewa Wani Yaro Idanu A Zariya

0
1364

Rabo Haladu Daga Kaduna

Wani yaro dan shekarau hudu a karamar
hukumar Zariya ta jihar Kaduna ya fada
hannun wasu wadanda ake kyautata zaton
masu ayyukan tsafi da sassan jikin
bil\’adama ne.
Abin da ya jefa yaron cikin tsaka mai wuya,
saboda matsafan sun kwakwale masa idanunsa
biyu.
Iyayen yaron sun ce ya ci karo da wasu
wadanda ake kyautata zaton matsafa ne
wadanda suka kai shi wani kango, da karfi
kuma suka kwakwale masa idanuwa guda biyu.
Yaron ya fada hannun matsafan ne a yayin da
ya fita daga gidan su a Unguwar Ban Zazzau a
Zariya don zuwa gidan makwabta.
A yanzu dai yaron yana kwance rai a hannun
Allah a wani Asibiti a Zariya, ba tare da
idanuwan sa guda biyu ba.
Ana zargin masu neman sassan jama\’a don tsafi
ko \’yan aiken su da tafka irin wannan ta\’asa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here