mutane 10 sun mutu 30 suka jikkata

0
1476

Rabo Haladu Daga Kaduna
Akalla mutane 10 sun rasu a yayin da wasu
sama da 30 suka jikkata sakamakon hare-
haren kunar bakin wake da aka kai a
wurare uku a garin Chibok na jihar Borno.
Ana zargin \’yan Boko Haram da kaddamar da
wadannan hare-haren.
Bayanai sun ce an tayar da bam guda a
kasuwar garin da kuma daya a wurin binciken
ababen hawa.
\”Akalla mutane 10 sun rasu, a yayin da fiye da
30 suka samu raunuka,\” in ji Ayuba Chibok.
A garin na Chibok ne a 2014 aka sace \’yan
mata dalibai su sama da dari biyu, wadanda
har yanzu ba aji duriyar galibin suba. Malam
Ayuba wani dan garin na Chibok, wanda ya ce
duk da ba ya cikin garin a yanzu, amma yana
da bayani kan abin da ya faru:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here