Kotu Ta Tsare Malamin Jami\’a A Kaduna

0
1521

A kokarin da ake yi na ganin an tsarkake daukacin kasar nan daga yan yada bayanai da za su tayar da husuma ba gaira ba dalili wata kotu a kaduna da tsare malamin jami\’a John Dan Fulani,har sai ranar Tilinin daya ga watan Fabrairu.

Shi dai John Dan Fulani ga duk masu hulda da kafafen sada zumunta musamman facebook da mu a nan kasar shi muka sani da kuma mu\’amalla yasan ko waye Dan Fulani,musamman wajen haifar da rudu da kokarin yada bayanan da ba za su amfani jama\’a ba.

Babbar matsalar ita ce shi wannan mutum a matsayinsa na masani mai karantar wa a jami\’ar jahar kaduna bai dace a same shi da yin irin wannan kalamai ba musamman ma har ya rubuta a shafinsa na yanar gizo wanda ba bu wanda zai iya hana lamarin yaduwa a cikin duniya,kuma shi dai bai yi kama da wadanda za a yaudare su asa su yi abin da bai dace ba kamar yadda al\’adar Najeriya take a rika yin amfani da yan baranda ko yan banga a haifar da matsaloli a kasa.

kamar dai yadda wasu masana ke ta kokarin bayyana wa cewa lallai ya dace a koya wa wannan malami na jami\’a darasi domin masu hali irin nasa su koya su kuma shiga hankalinsu saboda koda za a yi irin haka to ba kamar sa bane ya kamata a samu da wannan aikin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here