Makarantar haddar Alkura\’ani ta Madinatul Ahbab ta yaye dalibai 37

0
1811

Isah Ahmed Daga Jos

Makarantar haddar karatun Alkura\’ani mai girma ta Madinatul Ahbab da
ke garin Kwaftara kusa da garin Saminaka a karamar hukumar Lere da ke
jihar Kaduna, ta gudanar da bikin walimar ya ye dalibanta guda 37 da
suka haddace karatun Alkura\’ani mai girma a karshen makon da ya
gabata.

Da yake jawabi a  wajen taron Shugaban Makarantun  Madinatul Ahbab na
kasa Sheikh Falalu Dan Almajiri,  ya bayyana cewa ya zama wajibi  duk
musulmin duniya ya yi farin ciki da wadannan yara  da aka yaye a
wannan makaranta.

Ya ce a kalla muna da irin wadannan  makarantu guda 360 a Nijeriya da
kasashen makota, kuma muna tafiya da zamani a wadannan makarantu.

Ya ce muna da daliban da muka tura   kasashen Masar da Sudan da
Malesiya  wadanda suke  karatu a jami\’o\’i daban daban.

\’\’Babban burinmu shi ne mu baiwa yaran al\’ummar musulmi  kyakyawar
tarbiya domin su zamanto masu amfani ga al\’umma gabaki daya. Don haka
muna kira ga al\’ummar musulmi kan su baiwa irin wadannan makarantu
goyan baya da hadin kai, saboda irin alherin da suke haifarwa
al\’umma\’\’.

A nasa jawabin Shugaban Makarantar ta Madinatul Ahbab da ke Kwaftara
Alhaji Adamu Halilu ya bayyana cewa sun   shirya wannan taro ne domin
mu taya dalibansu  murnar haddar karatun Alkura\’ani mai girma da suka
kammala.

Ya ce a bana mun sami mahaddata da suka haddace karatun Al\’kura\’ani
mai girma kuma   muka  yayesu guda  37. Ya ce mun ya ye dalibai
mahaddata karatun Alkura\’ani mai girma da dama a wannan makaranta
domin  wannan ya ye dalibai shi ne karo na 25.

Ya ce babban burinmu shi ne mu cewa wannan makaranta ta bunkasa, don
haka  yanzu muna nan muna cigaba da ginin mazaunin wannan makaranta na
dindin.

Ya yi  kira ga iyayen yaran wannan makaranta  su taimaka  wajen biyan
kudaden makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here