yan fim din hausa na gogayya domin fitar da tauraro

0
3343

Rabo Haladu Daga Kaduna Ali Nuhu da Sadiq Sani Sadiq da kuma Adam
A. Zango ke gogayya da juna a matsayin
jarumin jarumai na fina finan Hausa.
Hakan ya bayyana ne a walimar bikin bayar da
kyaututtuka na Kannywood Awards wanda a ka
yi a Kaduna a daren Asabar.
A bangaren jarumai mata kuwa, Jamila Na gudu
da Nafisa Abdullahi da kuma Rahma Sadau, ne
ke gogayya da juna wajen neman matsayin
jarumar jarumai.
A Walimar wacce ta samu halartar masu ruwa
da tsaki a shirin fina-finan Hausa, an bayyana
jerin sunayen wadanda za su ci kyaututtukan
gwarzon shekara a bikin bayar da kyaututtuka
na Kannywood Awards.
Sauran rukunin da a ka fitar da sunayen
gwanaye uku-uku sun hada gwarzon fim, na
shekara da sauransu.
A hirarsa da manema labarai shugaban shirya bikin Dr.
Ahmed Sarari ya ce, alkalai ne su ka zabo
mutanen uku ddatabaseaga kowanne rukunin shirin
fina-finan, da aka kuma bayyana su a walimar da
aka yi.
Cikin wadannan ne a cewarsa, za a mikawa
mutum guda kyautar a jarumin ko jaruma a
bikin da za a yi a ranar 12 ga wanta Maris a
Abuja.
A shekarar da ta wuce ne Sadiq Sani Sadiq ya
zama jarumin jariumai, yayin da Rahma Sadau
ta zama Jarumar Jarumai.
Ko za su ci gaba da rike wannan matsayi a
wannan shekara?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here