\”Yan Majalisa A Jos Za Su Tunkari Batun Matsalar Rashin Ruwan Sha

  0
  1041

  Isah Ahmed, Daga  Jos

  MAJALISAR dokokin jihar Filato ta kafa kwamitin da zai  binciki matsalar rashin ruwan sha da ake fama da shi, a garin Jos da kewaye.
  Majalisar dokokin  ta kafa kwamitin da zai binciki wannan matsala ne, bayan da dan majalisar dokokin jihar  mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa maso Arewa, Honarabul Ibrahim Baba Hassan ya gabatar da wannan kuduri a gaban majalisar.
  Dan majalisar ya yi bayanin cewa al\’ummar Jos da kewaye suna cikin mawuyacin hali sakamakon wannan matsala ta karancin ruwan sha. Ya ce wannan matsala ta faru ne sakamakon gazawar gwamnatocin da suka gabata.
  \’\’A halin da ake ciki a kullum za ka ga yara kanana da mata suna fita daga gidajensu tun karfe hudu na asuba, don neman ruwan da za su yi amfani da shi a gidajensu\’\’.
  Ya ce abin takaici ne ganin irin makudan kudaden da gwamnatocin baya suka kashe tun daga lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya zuwa yanzu, don magance wannan matsala amma babu wani sakamako na alheri da
  aka gani kan wannan  matsala.
  Ya yi kira ga sabuwar gwamnatin jihar Filato ta kawo wa al\’ummar Jos dauki kan wannan mawuyacin hali da suke ciki, na karancin ruwan sha.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here