Za Su Bayar Da Dala Miliyan 250 Don Ci Gaba Da Yakar Boko-Haram

0
1079

Daga Usman Nasidi

WANI taron kasashe masu bayar da gudumawa ya yi alkawarin bayar da Dala Miliyan 250 domin yaki da kungiyar Boko Haram.
An yi alkawarin bayar da kudin ne a hedikwatar kungiyar Tarayyar Afirka, AU wanda Kasashen masu bayar da gudumawar sun hada da Amurka da kungiyar Tarayyar Turai da kuma kasashen Afirka.
Hakan na zuwa ne \’yan kwanaki bayan da hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane sittin da biyar sakamakon harin da aka kai a garin Dalori na jihar Borno.
NEMA ta kara da cewa akalla mutane 136 ne suka samu raunuka sakamakon hare-haren da ake zargin \’yan Boko Haram ne suka kai.
Sai dai a martanin da ta mayar, fadar shugaban kasar Najeriya ta ce harin da aka kai a kauyen Dalori ba zai kawar da maganar da shugaban kasar ya yi cewa sojojin kasar sun karya-lagon kungiyar ba.
Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 18,000 a yayin da wasu fiye da miliyan uku suka rasa muhallansu.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here