ba zan amincewa yan damfara da sunan boko haram ba

0
1126

Rabo Haladu Daga Kaduna
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
shaidawa manema labarai cewa ba zai yarda \’yan
damfarar da ke amfani da sunan Boko
Haram su yaudare shi ba.
Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a hirarsa
da manema labarai abirnin London, bayan ya hallaci taron
neman agaji ga \’yan gudun hijirar Syria.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne bayan da
wasu mutane ke fitowa suna cewa za su shiga
tsakanin gwamnati da Boko Haram domin a
saki \’yan matan Chibok sama da 200 wadanda
kungiyar ta sace a shekarar 2014.
Shugaba Buhari ya kara da cewa tattalin
arzikin kasar nan ya fada mawuyacin hali ne saboda
faduwar da farashin man fetur ya yi a
kasuwannin duniya.
Sai dai ya ce gwamnatinsa tana duba wasu
hanyoyin domin samun kudin-shiga.
Shugaba Buhari ya ce ba zai rage darajar Naira, ba, yana mai cewa babu wata
shaida da ke nuna cewa tattalin arzikin kasa,
zai bunkasa idan aka rage darajar naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here