Dan Kasuwa Ya Bindige Dan Fashi A Tafa

  0
  1338

  Daga Usman Nasidi

  WANI Dan fashi ya rasa ransa lokacin da suka kai hari gidan wani dan kasuwa a garin Tafa da ke karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.

  Garin Tafa wanda ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ayyukan barna sun sake dawo masa a ’yan kwanakin nan, bayan da gwamnatin jihar ta samu nasarar dakatar da su a baya.

  ’Yan fashin sun kai hari ne gidan wani fitaccen dan kasuwa a garin a karo na biyu, sai dai harin wanda ya auku a ranar Talata da ta gabata, an ce dan kasuwar mai suna Alhaji Muhammad Umar Zaro wanda aka ce ya nemi daukin ’yan sanda a lokacin harin ba tare da nasara ba inda ya hallaka daya daga cikin ’yan fashin, lokacin da yake yunkurin shiga masa gida.

  Wani makwabcin dan kasuwar da wakilinmu ya zanta da shi, ya ce ’yan fashin sun isa unguwar da misalin karfe 3:00 na dare ne a ranar. Ya ce sun yi ta yin harbe-harben bindiga lokacin da su ka iso.

  Daga nan suka yanke wayar kariya a wani sashi na katangar gidan dan kasuwar inda daya daga cikinsu ya kutsa kai ta cikin silin din wani dakin gidan.

  Ya ce wani daga cikin ’yan fashin sai ya yi yunkurin haurawa gidan, inda mai gidan ya harbe shi da bindiga ya fado waje ya mutu nan take.

  Bayanai sun ce ganin haka sai sauran ’yan fashin suka hanzarta barin unguwar, daga baya sai ’yan sanda suka shiga unguwar da mota suna jiniya, suka je gidan da ke daya daga cikin layukan da masu tu’ammali da miyagun kwayoyi ke gudanar da harkarsu a fili.

  Majiyarmu ta ce ’yan sandan sun wuce da gawar dan fashin zuwa ofishinsu tare da kama wani mutum a kusa da wajen, inda suke gudanar da bincike a kansa.

  Wakilinmu bai je babban ofishin ’yan sanda na garin don jin ta bakin DPO dinsu a kan al’amarin ba, saboda a baya lokacin da ya tuntube shi kan dawowar ayyukan masha’a a garin Tafa, ya yi masa kashedin kada ya sake zuwa ofishin. Sai dai majiyoyi da dama da suke da alaka da ’ya sanda, sun tabbatar da faruwar lamarin.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here