sata a jahar zamfara mutane 23 sun rasa Sara safe Sara data data Sara says

0
1707

Rabo Haladu Daga Kaduna Mutane 23 ne kawo yanzu, aka tabbatar da
mutuwarsu a harin da \’yan bindiga suka kai
kan kauyen Kwana da ke Zamfara.
Wani jami\’i a yankin ya ce an yi jana\’izar
mamatan, yayin da mutum guda da ya samu
rauni ke jinya a asibiti.
Maharan wadanda ake zargin barayin shanu ne,
sun afkawa kauyen ne a daren Asabar, a
lokacin da mazauna kauyen ke barci.
Dan majalisar da ke wakiltar yankin karamar
hukumar Maru a majalisar wakilan Najeriya, ya
shaida wa manema labarai cewa maharan ba su fuskanci
wata turjiya ba a yayin harin, kasancewar babu
jami\’an tsaro a yankin, har suka gudu.
Hon. Abdulmalik Zubairu ya zargi gwamnatin
Jihar ta Zamfarza da rashin ba wa matsalar tsaro a yankin
kulawar da ta kamata.
A shekarar da ta wuce gwamnatin tarayya ta kafa
wata runduna ta musamman domin yaki da
masu satar shanu a jihohin arewacin N\’ijeriya da
aka fi sani da \’Operation sharar daji\’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here