An Kai Wa Kamfanin Iskar Gas Mallaka Italiya Hari

0
1236

Rabo Haladu, Daga Kaduna.

WASU  da ake zargin masu tayar da kayar baya ne a yankin Naija-Delta, sun kai hari a wata tashar iskar gas a yankin.
Kakakin sojin Najeriya a yankin, Kyaftin Lazaru Eli ya ce maharan sun kai harin ne a tashar da ke kauyen Akala a karamar hukumar Ahoada ta jihar Ribas shekaranjiya Lahadi.
Tashar iskar gas din mallakar kamfanin Eni na Italiya ne. Tun bayan da hukumomi a Najeriya suka bada sammacin tsohon shugaban masu tayar da kayar  baya a Naija Delta, Government Ekpemupolo, wanda ake kira Tompolo, ake
samun karin hare-hare kan butunan mai a yankin.
Hukumar EFCC na zargin Tompolo da karkatar da Naira Biliyan 34 a wata kwangila ta tsaro domin kare butunan mai a yankin Naija-Delta, kodayake ya musanta zargin. Tompolo ya kasance daya daga cikin shugabannin masu tayar da kayar baya a yankin mai arzikin man fetur, kafin ya amince da yarjejeniyar afuwa da gwamnati ta yi musu a shekara ta 2009.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here