Kasafin Kudi Na 2016: Majalisa Ta Kara Wa\’adin Kammala Aikinsa

0
1315

Rabo Haladu, Daga Kaduna.
TANA kasa tana dabo game da aringizon da aka yi wa kasafin kudin Nijeriya, lamarin da ya sa kwamitin majalisa ya dage ranar kammala aikin na kasafin kudin da gwamnatin Najeriya ta aika masu..
A jiya Talata ne kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawan da na wakilai ya sanar da dage lokacin da zai kammala aiki a kan kasafin na shekarar 2016.
\’Yan majalisar sun ce hakan ya zama dole saboda abin da suka kira kura-kurai masu yawan gaske da ke kunshe a cikin kasafin.
An dai gano cewa an yi aringizon kudade a kasafin, ga misali Ministan ma\’aikatar lafiyar, Isaac Adewole ya ce an sauya baki dayan kasafin da ya bayar.
Sanata Danjuma Goje, shi ne shugaban kwamitin Majalisar dattawa mai kula da kasafin kudi, kuma ya shaida wa manema labarai cewa fadar shugaban kasar ta amince cewa akwai kura- kurai a kasafin.
Yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin manyan abubuwa uku da gwamnatin shugaba Buhari ta yi wa \’yan Najeriya alkawari.
Kuma wasu masana na ganin warware wannan matsala ta aringizo tana da muhimmancin gaske, ganin yadda tattalin arzikin kasar ke cikin mawuyacin hali, ga kuma fatan \’yan Najeriya na ganin an yi masu ayyukan da za su
inganta rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here